BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
Takaitaccen Bayani Kan Madina
Garin Yathrib (ko kuma Madina) gari ne da ke tsakiyar sahara da ake da koramai da rijiyoyi masu yawa, bishiyoyin dabino da sauran itatuwan marmari kuma sun kewaye garin. Yana kimanin kilomita 450 daga arewacin garin Makka. Kabilun larabawa nan masu bautar gumaka, wato Aus da Khazraj, su suka mamaye garin. Haka kuma akwai wsu kabilun Yahudawa kamar su Bani Kuraiza, Bani Mugir da Bani Kainuka da suka yo hijira zuwa garin Madina don jiran Annabin karshe da zai zo kamar yadda suka karanta a cikin tsoffin littattafansu. Amma akwai mummunar gaba tsakanin wadannan kabilu biyu masu bautar gumaka (Aus da Khazraj), wanda hakan ya haifar da yakoki da lalata dukiyar juna a tsakaninsu. Bugu da kari kuma babu jituwa tsakanin wadannan larabawa da wadancan yahudawa: domin su Yahudawan na amfani da littafansu suna yin izgili ga wadannan masu bautar gumaka na cewa da sannu wani Annabin Allah zai bayyana a cikin Larabawa kana kuma ya zo garin Madinan, kuma zai kawo karshen wannan mummunar hanya tasu.
Amma abin mamaki lokacin da Manzon Allah (s) ya bayyanar da annabcinsa kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, wadannan kabilu na Larabawa, wato Aus da Khazraj, su ne suka bar bautar gumaka suka karbi Musulunci, amma wadancan Yahudawan da kakanninsu suka yi yo hijira saboda jiran Manzon Allah (s), sun ki karbar wannan sako na Musulunci.
Dalilinsu dai shi ne shi Manzon Allah (s) balarabe ne da ya fito daga tsatson babban dan Annabi Ibrahim (a.s), wato Annabi Isma'il (a.s), don haka bai zama karbabbe ba a wajen yahudawa.
A wani bangaren kuma wannan hijira ta Manzon Allah (s) zuwa gari Madina ta sa kabilun Aus da Khazraj sun tuna da abubuwan da Yahudawan nan kr fada masu dangane da Annabi (s), don haka cikin gaggawa suka karbi sakon Musulunci, wanda hakan ya kawo karshen mummunar gabar da ke tsakaninsu. Allah Madaukakin Sarki Ya cika zukatansu da kaunar juna wadda a da ba su taba samun irinta ba, Ya kuma hada su karkashin tutar Musulunci mai girma.
Amma su wadancan yahudaw, cikin tsananin gaba,sai suka juya wa Manzon Allah (s) baya kamar yadda suka yi wa Annabi Isa (a.s) a karnoni shida da suka wuce.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved